Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta ce masu amfani da Intanet a kasar nan sun karu da Miliyan 143 da dubu 63 zuwa miliyan 151 da dubu 51, a zango na biyu na shekarar da ta gabata.
Wanda hakan ke nuna cewa an samu karin kashi 4 da digo 59 na masu amfani da Intanet a fadin kasar.
Bisa kididdigar da aka fitar ya nuna cewa jihar Legas ta fi yawan masu aikewa da sakon murya ta kafar Intanet, sai jihohin Kano da Ogun.
Hukumar NBS ta tabbatar da cewa jihar Bayelsa da Ebonyi su ne suke matakin karshe na masu amfani da Intanet a fadin kasar.