- Wani dan Najeriya ya koka kan sauyin da matarsa ta yi masa shekaru biyu bayan sun koma Birtaniya
- Ya ce ya ɗauki nauyin karatunta na aikin jinya a Najeriya kuma sun yi hijira zuwa Turai bisa takardar izinin aiki.
- Daga ganin ta fara samun ƙarin kuɗi kawai sai ta canza halayanta a kai na.
Wani dan Najeriya ya kasance cikin ruɗani sakamakon canjin hali da matarsa ta yi bayan sun koma kasar Birtaniya.
Lauyan kare hakkin bil’adama Oloye TD wanda ya rubuta labarin mai ratsa jiki a shafin Twitter ya ce ya samu kira daga Swancome a Burtaniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata ƴar shekara 71, wacce tayi aure tana da shekara 50, yanzu haka ta haihu.
A cewarsa , mijin da matar sun shafe shekaru 14 suna tare kuma ya ɗauki nauyin karatunta na aikin jinya a Najeriya, bayan ta kammala karatun digiri na biyu.
Ya ce sun je Burtaniya ne bisa takardar bizar aiki, shi kuma a matsayin wanda yake a ƙarƙashinta, daga nan ne aka fara samun matsala.
Mutumin ya ba da labarin cewa matarsa ta canza lokacin da ta fara samun kuɗi fiye da na shi, ya kuma ƙara da cewa tana ɓoye kuɗinta ba ta bashi ko sisi.
Ya ce al’amuransu ya tsananta ga kuma rikicin cikin gida wanda hakan ya sa iyayensu shiga ciki.
Sai dai ya ce matarsa bata canza daga kyaun da take da shi ba, kuma zai yi mamakin ganin cewa tana aikawa iyayenta kuɗi a Najeriya domin su gina mata gida.
Ga wasu daga cikin ra’ayoyin da waɗan da suka bibiyi labarin a shafukan sada zumunta:
@saintshedrack ya ce: “Aure na baya-bayan nan da aka yi a Najeriya a kaso 99.9 anyi ne don kuɗi ba soyayya ba. A lokacin da mutane ke fafutukar ganin an samar da shugabanci na gari wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa, kyakkyawan shugabanci a wurare irin su Amurka da Birtaniya na fallasa wadannan batutuwa.”
@MizNma27 ya ce: “Saboda ya ɗauki nauyin karatun ta, hakan na nufin ya cancanci albashinta? Iyaye su dinga saka ido ga albashin ‘ya’yansu ma idan haka ne. Me ya sa yake sa ido a cikin kuɗinta?
@timosilver: “A lokacin da nake ƙaramin yaro, mun ziyarci ƙauyenmu a lokacin Kirsimeti kuma na sami damar yin magana da Babana ya kuma ce da ni, “Duk abin da ka yiwa mace, ɗauka kamar ka shuka dusa ne kawai. “Ban manta da hakan ba.”