Yayin da hada-hadar kasuwancin intanet din nan na Crypto ke ci gaba da cin karensa babu babbaka, jama’a da dama harkar ta zamo musu gobarar titi a Jos, yayin da wasu kuwa suka fada komar yan bani mu samu.
Wata kila bisa irin rahotanni da muka harhado mu gano cewa daya daga cikin mutane da al’amarin bai musu dadi ba har da direban tsohon Sanata daga Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani.
Kamar yadda Sanatan ya wallafa a shafinsa na Tuwita, lamarin har ya kai ga ya dakatar da direban nasa na mako guda don bashi hutu ya maido da jinin jikinsa sakamakon wannan tataburza.
Kamar yadda Shehu ya bayyana cewa a yanzu haka shi ke tuka kansa don samun kwanciyar hankali da kuma gudun abinda ka iya biyowa baya Sakamakon tunani da direban nashi zai iya wanda na daga cikin dalilin da ya sa ya dakatar da shi daga tukin.
Ko sa yake bai ambaci sunan shi ba, to amma dai mafiya yawan attajira, yan siyasa ko kuma masu kudi kamar wannan, ba sa iya tara direba fiye da mutum guda da zai rika tuka su na musamman.