Wani magidanci ya nuna damuwar sa kan yadda matar sa bata nuna masa kulawa.
Magidancin ya koka da cewa kwata-kwata matarsa bata nuna tana kishin sa, wanda hakan yana matuƙar ci masa tuwo a ƙwarya.
Magidancin wanda ya nemi a sakaya sunan sa dai, ya bayyana damuwar tasa ne a wata wasiƙa da ya rubutowa shafin Northern Hibiscus wanda ke haɗa aure da ba ma’aurata shawarwari a Facebook.
KU KARANTA KUMA: Har yanzu ina ƙaunar su” Cewar matashiyar da ƴan Chana suka sace tana jaririya
Yace ya san cewa matarsa tana ƙaunar sa amma ko kaɗan idan aka zo ɓangaren kishi, to ba abinda ke sha mata kai, wanda hakan ke tayar masa da hankali.
A cewar sa duk wasu abubuwa da mata ke yi domin nuna kishi kan mazajen su, irin su duba wayar sa, idan ya daɗe bai dawo gida a turke shi sai an ji ba’asi, babu wanda take yi daga ciki.
Yace hakan ya sanya gabaɗaya guiwoyin sa sun sare, yake jin kamar tana nuna masa cewa shi ɗin ba kowan kowa bane.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su, ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
Rukayya Ango ta rubuta:
“Ƴar albarka na kula baku san ma me kuke so ba . Ta burgeni kwarai. Da duba waya kadai takeyi da yanzun an ishemu da zance iri-iri.”
Zainab Ishaq Muhammad ta rubuta:
“Au to mutum sai ya tsaya kishi ya kashe shi, tabbb, ai in mutum yai dai-dai ya sani, in ma bai yi ba ya sani. Me ye nawa? kai ta kulawa.”
Abubakar Lawal ya rubuta:
“Ai shi namiji haka wasu matan suke dafa su cikin ruwan sanyi yasin, yanzu da fada takeyi kuma sai kaji haushi ko?”
Mazan Najeriya Kwata-Kwata Ba Su San Yadda Ake Soyayya Da Mata Ba -Wani Matashi
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya bayyana mazan Najeriya a matsayin waɗanda ba su san yadda ake sace zuciyar mata ba.
Wani matashi ɗan Najeriya a shafin Twitter ya bayyana cewa da yawa daga cikin mazajen Najeriya ba su san yadda ake soyayya da mata ba.