Cike da takaici wata budurwa ƴar Najeriya mai rayuwa a birnin Jos, jihar Filato, ta bayyana abinda ya faru da ita bayan taje banki.
A cewar budurwar, taje bankin kasuwanci na First Bank domin ciro kuɗi inda aka bata ƴan ₦50 a kanta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari yayi matuƙar baƙin ciki da wahalar da ƴan Najeriya ke sha kan sababbin kuɗi -Minista
Abin takaici bayan ta koma gida, sai ta duba kuɗin taga duk sun lallace sun koma yagaggu.
Ta roƙi ƴan Najeriya da su kawo mata ɗauki, inda ta ƙara da cewa ba wani mai kasuwancin da zai karɓi waɗannan kuɗin a hannun ta.
A kalamanta:
“Barkan mu da safiya. Wannan shine abinda ma’aikatan banki suka zauna suka tattara. Ina yin wannan bidiyon ne daga Jos, jihar Filato. Ku taimakeni ƴan Najeriya. Ina muka dosa ne? Wannan itace rayuwar? Dan Allah ku taimakeni. Ko masu keken Napep ba zasu ƙarɓi wannan kuɗin ba.”
https://www.instagram.com/p/CoKlqv7uyJt/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan bidiyon da budurwar tayi. Ga kaɗan daga cikin waɗanda jaridar Dimokuradiyya ta tattaro:
Belle_beauty_lounge ta rubuta:
“Ah! meyasa kika karɓa ne?”
Adankem.best ya rubuta:
“Ƴan Najeriya ne suka mayar da kuɗin suka zama haka, ba laifin bankin bane. Idan har ba ƴan Najeriya sun koma mutunta takardun kuɗi ba, za a cigaba da samun matattun kuɗi.”
Chefmimii ta rubuta:
“Ban taɓa jin cewa yakamata na bar ƙasar nan ba sai jiya. Ba man fetur, ba wutar lantarki, ba kuɗi, idan an turo kuɗi basu zuwa. Kaje kan kanta cirar kuɗi ka kwashe dogon lokaci a layi daga ƙarshe a baka matattun kuɗi.”
An Kuma: Wani Mutum Ya Faɗi Matacce a Layin Cirar Kuɗi a Banki
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya mutu akan layin cirar kuɗi a banki.
Wani abun ban takaici ya sake aukuwa inda wani mutum ya faɗi ya mutu a cikin banki a yayin da yake ƙoƙarin ciro kuɗi.
Lamarin ya auku ne wani bankin kasuwanci dake a Agbor, jihar Delta, a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Mutumin wanda ba a san kowane ne ba, ya faɗi ya mutu ne bayan ya kwashe dogon lokaci akan layin cirar kuɗi a bankin.