Wani abun ban takaici ya sake aukuwa inda wani mutum ya faɗi ya mutu a cikin banki a yayin da yake ƙoƙarin ciro kuɗi.
Lamarin ya auku ne wani bankin kasuwanci dake a Agbor, jihar Delta, a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Mutumin wanda ba a san kowane ne ba, ya faɗi ya mutu ne bayan ya kwashe dogon lokaci akan layin cirar kuɗi a bankin.
KU KARANTA KUMA: Wata mata mai juna biyu ta mutu bayan mijinta ya kasa ciro kuɗi a banki
Mutumin ya mutu ne a cikin harabar bankin, a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairun 2023.
Majiyoyi masu ƙarfi tare da shaidun gani da ido sun tabbatarwa da shafin Linda Ikeji aukuwar lamarin.
Wani daga cikin majiyoyin mai suna Omole Mike, ya sanya hoton mamacin a shafin Facebook inda ya rubuta:
“Yanzun nan da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana. Wani mutum ya faɗi ya mutu a cikin reshen bankin First bank of Nigeris na Agbor. Ya mutu ne a ranar 02-02-2023.”
Ƴan Najeriya na cigaba da fuskantar halin matsi da takura a dalilin sauya fasalin kuɗin naira da babban bankin Najeriya (CBN) yayi.
A yayin da mutane suka kwashe ƴan kuɗaɗen suka kai bankuna, yanzu kuma ya zama wani aiki ja mutum ya samu sababbin kuɗaɗen da zai yi amfani da su.
Hakan ya sanya aka samu dogayen layuka a wajen ciro kuɗi a bankunan ƙasar nan.
Shugaba Buhari yayi baƙin ciki matuƙa da wahalar da ƴan Najeriya ke sha kan sababbin kuɗi -Minista
A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya damu matuƙa da halin da ƴan Najeriya suka shiga saboda sababbin kuɗaɗen naira.
Ministan kuɗi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa shugaba baya jindaɗin wahalar da ƴan Najeriya ke fuskanta saboda sababbin kuɗaɗen naira.
Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne yayin da take magana a wajen wani taron ministoci a faɗar shugaban ƙasa.