- Majalisar dokokin Ribas ta kada kuri’ar yin watsi da matakin da gwamna Sim Fubara ya dauka
- Kada kuri’ar tasu ta zo ne lokacin da wasu ‘yan majalisar da ke biyayya ga Ministan Birnin Tarayya suka yi yunkurin tsige Gwamnan Jihar Fubara
- Wannan na Zuwa ne kan wasu dokoki hudu da ‘yan majalisar suka zartar
Majalisar dokokin jihar Ribas ta kada kuri’ar yin watsi da matakin da gwamna Sim Fubara ya dauka na hana su furuci kan wasu dokoki hudu da ‘yan majalisar suka zartar.
Dokokin sun hada da Gudanar da Kudaden Jihar Ribas da Dokar Bayar da Cin gashin Kai na Kudi ta 2023, Dokar Gyaran Kananan Hukumomin Jihar Ribas 2023, Tallace-tallacen Jihar Rivers da Amfani da Dokar gyaran Kaddarorin Mallakar Jiha 2024, da Dokar Gyaran Sarakunan Gargajiya ta 2024.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: An Yanke Wa Bishop Hukuncin Daurin Rai da Rai Bisa Wasu Tuhume-Tuhume
Kada kuri’ar tasu ta zo ne lokacin da wasu ‘yan majalisar da ke biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike suka yi yunkurin tsige Fubara.
Hakan ya biyo bayan rikicin gwamnan da Wike kan kula da tsare-tsaren siyasa da albarkatu a jihar Ribas.
Ana cikin zazzafar rikicin ne wasu ‘yan majalisar dokokin jihar suka sauya sheka zuwa jam’iyyar (APC) domin nuna goyon bayansu ga Wike.
Sai dai shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani a lamarin inda ya yi galaba akan Wike da Fubara suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Jurgen Klopp Zai Sauka Daga Matsayin Kocin Liverpool
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, zai yi murabus daga aikinsa a karshen kakar wasa
Klopp ya zama kocin Reds a watan Oktobar shekarar 2015
Wannan dai ya nuna tafiyar Klopp a Matsayin wata alama ce ta ƙarshen zamani a Liverpool
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, zai yi murabus daga aikinsa a karshen kakar wasa ta bana.
Klopp ya zama kocin Reds ne a watan Oktobar shekarar 2015 kuma kwantiraginsa zai kare har zuwa shekarar 2026.