Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta sake tsarin buga wasannin sada zumunta data sanya zata fafata a watan gobe wato watan Oktoba kenan na shekarar 2020, an sake tsarinne a jiya Juma’a, Najeriya dai ta kwashe watanni da dama ba tare data fafata wasan sada zumunta ba inda tun lokacin da cutar Coronavirus ta shigo basu fafata ba.
Da dai Najeriya ta bayyana cewar zata fafata wasanni guda biyu na sada zumuntar da ƙaaashen Ivory Coast da kuma Tunisia, amma sakamakon janyewa da ƙasar ta Ivory Coast tayi wato ta fasa bugawa da Najeriya yasa aka sauya sunan wata ƙasar maimakon hakan.
A yanzu dai Najeriya zata fafata wasannin guda biyu da ƙasashen Tunisia da Algeria a sabon watan mai kamawa na Oktoba, ita dai ƙasar Algeria itace ta maye gurbin ƙasar Ivory Coast kenan a daren na jiya da labarin ya canza a kan wasannin sada zumuncin.
A yanzu dai anyi ittifaƙin cewar babu wata ƙasa a nahiyar Afrika data kai Najeriya matasan ‘yan wasa masu hazaƙa da ƙwazo kuma masu ƙananan shekaru musamman idan akayi la’akari da irin gudun mawar da suke bayarwa a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suke buga wasanninsu, domin kusan kowannensu yana daga cikin 11 na farko da ake fitowa dasu a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan nasu.
A cikin wannan watan dai Najeriya ta sake matsowa a matakin tsaiwar jaddawalin koaacce ƙasa a duniya inda a halin yanzu Najeriya na matsayi na 29 a duniya sannan kuma tana matsayi na 3 a nahiyar Afrika yayin da ƙasashen Senegal da Tunisia suke a matsayi na 1 dana 2.
Najeriya dai a ƙarƙashin mai horas wa Rohr tayi bajinta sosai a wasannin gasa daban-daban da kuma wasannin sada zumunta a iya tsawon shekarun daya kwashe tare da Super Eagles inda shima ya bayar da gudun mawa wajen sauya akalar wasan ƙungiyar ta Super Eagles.
Sai dai a wannan karon mai horas war ya fito da wasu sababbbin ‘yan wasa da zasu baiwa Super Eagles gudun mawa inda ake ganin cewar tabbas zasu iya ƙwatar waje wato wasu ‘yan wasan zasu rasa gurabensu a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Super Eagles ganin irin yadda sababbin matasan ‘yan wasan suke buga wasanni na ban sha’awa da ƙayatar wa.