Gwamnatin tarayya ta ce zuwa nan da a kammala gyare-gyaren da ake yi a bangaren kere-kere da kuma talla, Najeriya za ta samu dala biliyan biyu a tallace-tallace a cikin shekaru uku.
Ministan yada labarai da raya al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka a Abuja a wani taron fasaha na kwamitin tantance masu saurare da gwamnati ta kaddamar.
Lai Mohammed wanda ya ce a halin yanzu Naira miliyan 400 da Najeriya ke samu daga tallace-tallace, abin da ba za a amince da shi ba ne, daga nan sai ya nanata matsayin da yake fatan ganin an samu kaiwa zuwa Dala biliyan biyu cikin shekaru uku.
Ya ce idan aka kammala aikin yin garambawul, masana’antar kere-kere ba za ta sake zama kamar haka ba.
Ministan ya yaba da kokarin da kungiyar ta yi wajen samar da lokaci mai girma na wadata daukacin bangaren kere-kere.
“Abin da ya fi, idan ba kowa ba ne ko da yaushe ake buƙata shine filin wasa a cikin babbar ƙasarmu mai mutane fiye da miliyan 200, fiye da gidajen rediyo da talabijin 500, tare da akalla gidajen TV miliyan 24.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta taimaka da ka’idojin da ake bukata tare da bude kofa ga masu hannu da shuni domin samun nasarar yin garambawul.
A cewar Mohammed, gwamnati za ta samar da ingantaccen yanayin kasuwanci ga duk masu tallace-tallace da hukumomin kasa da kasa su gaggauta yin kasuwanci a kasar.
Shugaban kwamitin, Mista Tolu Ogunkoya ya gode wa ministan saboda hangen nesa da kuma sha’awar masana’antar da kuma kasancewarsa a taron fasaha.
Ya kuma ba da tabbacin cewa kwamitin zai yi aiki tukuru domin cimma burin da aka sa a gaba a watan Nuwamba domin kammala aikin.