Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya tana da karfin biyan bashin da ta ciyo domin gina hanyoyin jiragen kasa cikin shekara ashirin.
Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Chana ita ce kasa daya tilo da take biyan bashi da ribar kasa da kasha 2.8.
Ya tabbatar da cewa babu wata kasa a duniya da take bayar da ba shi ba tare da ta samun tabbacin cewa za a biya ta bashin da ta bayar ba.