Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya karyata rade-radin cewa ya amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi. Ya bayyana cewa irin wadannan bayanai kwata-kwata karya ne kuma na sharri ne. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Crusoe Osagie, ya fitar, gwamnan ya ce masu zagin sa ne ke yada wannan jita-jita da wata manufa ta daban da kuma yaudarar jama’a don son kai.
KATANTA WANNAN LABARIN: Malaman Jami’ar UNICAL 10 Ne Suka Mutu, Tun Bayan Fara Yajin Aikin Mu– Shugaban ASUU
Sanarwar ta kara da cewa, “Labarin da aka samu a wani sashe na kafafen yada labarai, na cewa gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, kwata-kwata karya ne da kuma sharri. Babu wata magana makamancin wannan da ta samo asali daga gwamnan.
“Masu zagi da wasu dalilai na daban ne ke yada labarin, da nufin yaudarar jama’a da kuma bata jama’a don son kai.”
Mai taimaka wa gwamnan ya ci gaba da cewa, “Gwamna Obaseki tun farkon zabukan fidda gwani ya kasance a sahun gaba wajen yakin neman zaben jam’iyyar PDP da dan takararta, Alhaji Atiku Abubakar da abokin takararsa Sen. Ifeanyi Okowa. .
“Obaseki a matsayinsa na jagoran jam’iyyar PDP a jihar Edo, zai tura dimbin magoya bayansa domin tabbatar da nasarar jam’iyyarmu da ‘yan takararta a babban zabe mai zuwa na 2023,” ya kara da cewa.
A WANI LABARI KUMA: Rundunar Hadin Gwuiwa Sun Kama Likitan Bogi, Bayan Wani Majinyaci Ya Mutu A Hannunsa
Rahotanni na nuna cewa, Rundunar hadin gwuiwa a jihar Bauchi ta kama wani likitan jabu bayan wani aikin tiyata da ya yi.
Daily Post ta ruwaito cewa, Wanda ake zargin mai suna, Andrew Godwin, wanda ya fito daga jihar Nasarawa, an kama shi ne a ranar Lahadin da ta gabata saboda wani aiki da yayi wnada bai yi nasara ba kuma ya kai ga mutuwar Joshua Haruna.