Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talatar , ya bayyana wani abin mamaki, inda ya ce shi maraya ne, bai san waye mahaifinsa ba, kuma ya yi shekara tara a makarantar kwana domin samun ilimin da ya ba shi damar shiga aikin sojan Najeriya. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a ranar Talata 27 ga watan Agusta a Damaturu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar Sin Ta Dakatar Da Baiwa ‘Yan Japan Biza
Shugaban a kokarinsa na karfafa muhimmancin ilimi ya bukaci dimbin jama’ar da suka hallara a filin wasan da su tabbatar sun tura ‘ya’yansu makaranta, yana mai jaddada cewa duk abin da suke da shi a duniya za a iya kwacewa sai dai a bar su ilimin da suka samu.
Da yake tallata takarar Tinubu da Shettima, shugaban ya ce kuri’ar da aka kada wa masu rike da mukaman jam’iyyar, zai tabbatar da samar da ci gaban da aka samu a bangaren tsaro, tattalin arziki da ilimi a kasar nan.
Buhari ya kuma yi amfani da yakin neman zaben da ya yi don tunkarar nasarorin da ya samu a kan ‘yan ta’adda a yankin, inda ya jaddada cewa gwamnatin APC a karkashinta ta yi namijin kokari fiye da kowane lokaci domin ta hanyar karya lagon duk wanda ke barazana ga hadin kan Nijeriya.
Yayin da yake jawabi ga jama’a da harshen Hausa, Buhari ya ba da labarin yadda ‘yan Boko Haram suka yi barna a kan al’umma da dukiyoyinsu da tattalin arzikinsu, kafin shiga tsakani da gwamnati ta yi inda tai ga halaka ‘yan ta’addan da sojojin Najeriya da jami’an tsaro suka yi.
“Ku tabbata kun tura ‘ya’yanku makaranta kuma ku fahimtar da su cewa duk abin da kuke da shi a duniya za a iya kwace muku sai dai ilimin da kuke da shi a kan ku.” Inji Buhari.
Sai ya kara da cewa: ‘‘Ni maraya ne; Ban san mahaifina ba. Na yi shekara tara a makarantar kwana kuma saboda ilimi [na] ya sa aka sa ni aikin sojan Najeriya.”
Ya gaya musu: ‘Ina so ku ƙarfafa bangaskiyarku, ku yi iya ƙoƙarinku don ku ɗaukaka ’ya’ya da iyalin da Allah ya ba ku amana. Kada ku ci amanar wannan amanar.”
A wani labari kuma, Tinubu, Gwamnonin APC, PCC Sun Sake Duba Dabarun Yakin Neman Zaben Jam’iyyar
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar da kuma wasu mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PCC.
Kazalika a taron da aka fara da yammacin ranar Litinin da kuma aka kammala da safiyar ranar Talata shi ma mataimakin dan takarar shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya halarta .