Tabbas abubuwan al’ajabi ba sa karewa kuma in har da ranka za ka sha kallo a fadin duniyar nan.
Malaman addinai sun dade suna yin abubuwan bamamaki, wasu su burge jama’a yayin da wasu suke sanya wa mutane tantama.
KU KARANTA: Makomar kiristoci na cikin hatsari a zaɓen 2023, Fasto
Akwai abubuwan da suke yi wadanda kan janyo musu mutunci a idon jama’a yayin da wasu ke zubar musu kima da daraja.
A wannan karon, Dimokuradiyya ta zo da wani labari mai banmamaki, al’ajabi tare da daure kai kamar yadda majiyarmu ta apahausa.com ta zo da shi.
Wasu hotuna ne suka bayyana inda aka ga wani fasto ya tashi sama wanda kamar yadda aka ruwaito ya sanar da mambobin cocinsa cewa zai tafi Aljanna ne.
Da alamu sun yarda da wannan maganar ta shi, wanda hakan yasa duk suka taru suka yi cirko-cirko.
Ba wannan kadai bane abinda yafi banmamaki, an ga yadda da yawansu suke yi masa bankwana da fatan alheri.
Tabbas wannan abin ya yi matukar daukar hankalin ‘yan soshiyal midiya wanda wasu ke ganin rainin hankali ne, yayin da wasu ke kallon hakan a abin ban al’ajabi.
Ko ma dai menene, Allah yasa mu dace kawai zamu ce.
Za’a Samu Barkewar Rikici Idan INEC Ta Dage Zabe — Fasto Ya Yi Gargadi
Shahararren mai wa’azin bishara a yankin Kudu maso Yamma, Samson Oluwamodede, ya yi hasashencewa za a samu sakamako maras kyau idan hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta yi yunkurin dage babban zaben da ke tafe. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Fita-da-iri, Oluwamodede ya yi gargadin cewa sauga zaben daga ranakun da aka tsara zai iya jefa kasar cikin rudani da tashin hankali.