Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu
Wai ya aka yi tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta zama jinin Sarauta? Kuma ta ina ta zama yar Sarauta?
Wannan ita ce tambayar da mutane su ke ta yi a lokacin da aka ji a kwanakin nan Mansurah Isah tana alakanta kan ta da Sarauta, inda ta ke kiran kanta da Gimbiya.
Wakilin jaridar Dimukaradiyya ya nemi jin ta bakin ta, don jin gaskiyar dalilin da ya sa ta ke Kira kan ta da Gimbiya, sai ta ce.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin a jiya
“To gaskiya wannan labarin na Sarauta ba wani sabon abu ba ne, na san da shi tun muna yara Maman mu tana ba mu labarin tana cewa, su ya yan sarakuna ne, ana yawo da su a kan Doki, kuma a lokacin su kadai ne suka samu ilimin zamani, ko zanen fuskar su ma a lokacin da za a yi musu, sai da aka dora su a kan Doki ana ta zagaya gari da su, don suna da wayon su aka yi musu sun je makaranta aka je aka dakko su a kan Doki, ana tafiya da su a kan Doki a cikin kasuwa sai mutane su ke ta sha’awar su, za a je a yi musu zanen jinin Sarauta, wanda a yanzu ma ba komai ba ne saboda sauyin yanayi haka ta ke ba mu labari” inji ta.
Ta ci gaba da cewar “Kuma Maman mu tana fada mana cewar, kakanta wanda ya haifi Mahaifin ta Shi ne Sarkin garin Iwo na Kasar Yarabawa a cikin jihar Osun, kuma a gidan su ne a ke nada Gimbiyoyi wato ya yan Sarki, wanda Nima da a can na taso Nima Gimbiya ce.To sai kuma shi kakan mu wanda ya haifi Maman mu da ya taso ba ya son Sarauta, shi ne sai ya dawo Kano da zama ya zauna a unguwar Fagge ya zauna, har ita Maman mu suka hadu da Mahaifin mu Alhaji Isah suka yi aure, ” a cewar ta
Kazalika ta ce, “To zawan da Sarkin Iwo na yanzu Kano a lokacin Bikin Yusif Buhari a nan muka hadu da shi, nake sanar da shi Nima asalin mu garin mu daya na fada masa asalin na, don haka sai ya yi mamaki ya ke cewa ai ke Gimbiya ce” inji Mansurah Isah
“To wannan ya sa aka ji ina alakanta kaina da Sarauta, kuma nan gaba zan je har garin mu, domin na gudanar da ayyukan Gidauniyar da na ke yi, don su ma su Sami irin ayyukan da muke gudanarwa. kuma ina fatan idan na je za a nada mun sarautar Gimbiyar da na Gada a wajen kakan Maman mu. “