Burtaniyar ta shirya taron koli kan saka jari tsakaninta da kasashenna Afirka a kokarin da take yi na neman sabbin abokan hulda gabanin ficewarta daga tarayyar EU karshen wannan watan.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da kasashen za su fi bai wa karfi har da noman gyada da Najeriya ta yi kaurin suna a kansa.
Alhaji Tajuddeen Aminu Dantata shi ne shugaban kamfanin Dantata Foods and Allied Products da ke Najeriya, kuma na daya daga cikin shugabannin kamfanonin da suka halarci taron daga Najeriya, ya shaida wa BBC cewa taron zai taimaka wajen samun masu siyan gyadar daga sassan duniya da kuma ita birtaniya wadde dama ita ce ke siyan yawancin gyadar da Najeriya ke samarwa.
Ya ce kamar a Najeriya an sanya kudurin noma akalla kadada dubu dari a kashin farko na shekarar 2020.