Masana harkokin tattalin arzikin duniya, sun ce kasar Nijeriya ta shiga wani garari sakamakon faduwar da farashin danyen mai ya yi saboda annobar Korona.
Masanan na cewa hakan ya sanya kasar da ta fi dukiya a Afirka gamuwa da barazanar da ba ta taba gani ba saboda dogaron da ta yi kacokaf a kan albarkatun man.
Koda yake hajar na iya farfadowa zuwa wani matsayi na farashi a kan kowace gangar danyen man a kasuwannin duniya, har yanzu da sauran aiki gaban Najeriyar ganin kusan kashi 90% na kudaden shiganta daga man ta dogara.
Ita ma ministar kudin kasar, Zainab Ahmed, ta fada a makon jiya cewar annobar COVID-19 da kuma faduwar darajar makamashin, sun taba Nijeriyar matuka.
Nijeriyar dai ta yi kasafin kudinta na bana ne a kan mizanin farashin man dala 57 a kan kowace ganga guda.
Rahoton DW Hausa