A yayin da Hukumar sadarwa ta Nijeriya wato NCC ta nemi da a daina sayarwa da wadanda ba su kai shekaru 18 layin waya ba, wanda NCC ta ce hakan ya dace da dokokin mallakar layin waya sashi na 70 na kundin bayanan sadarwar Nijeriya na shekarar 2003.
MTN ta bukaci NCC ta tsayar da shekara 14 a matsayin mafi kakantar shekarun mallakar layin waya a maimaikon 18.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa NCC ta dage akan cewa dole sai mutum ya kai shekara 18 kafin ya mallaki layin waya harda rajista a Nijeriya.
Idan ba ku manta ba, Dimokuradiyya ta labarto muku cewa Hukumar sadarwa ta Nijeriya, wato NCC ta haramta sayarwa da ‘yan ƙasa da shekarunsu bai kai 18 ba rajistan layukan waya.
Hukumar ta NCC ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta wallafa a shafinta, inda ta ce sai mutum ya kai shekara sha takwas za a rika yi masa rajistan layin waya.
A lokacin gabatar da wannan tsari a gaban masu ruwa da tsaki da kamfanonin sadarwa ciki harda MTN, inda kamfanin ya nemi a rage waɗannan shekaru.
Masha allah