Shugaban Ƙungiyar Ƴan Aware na tsagerun IPOB Nnamdi Kanu yace bai aikata laifun da ake zargin shi ba, wanda Gwamnatin Tarayya ta sake yin kwaskwari ma ga wata ƙara data shigar a kanshi.
A yau ne ya bayyana a gaban kotun Babbar Birnin Tarayya Abuja, akan ƙarar shi da akeyi na zagon ƙasa, da ta’addanci, wanda Gwamnatin Tarayya ta sake yin kwaskwari ma akan haka, ga ƙararraki guda bakwai da ake zargin shi da aikatawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na ganawa da Hukumomin Tsaro
Jim kaɗan bayan ya bayyana cewar bashi da laifi a yau, Babban Jojin ya bada umarnin a cigaba da tsare shi a kurkukun Hukumar Jami’an tsaron farin ta DSS, bayan anƙi yarda da buƙatar shi na mayar dashi a cibiyar gyaran aƙida.
An ɗage zama shari’ar zuwa 10 ga watan Nuwamba na Shekarar 2021