Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen jihar Katsina, ta kori mataimakinta dan takarar gwamnan jihar, Muttaqa Rabe-Darma, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Sani Liti, da wasu manyan jami’an gudanarwarta. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Daraktan a yada labarai na jam’iyyar NNPP, Alhaji Nasiru Usman-Kankia ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Katsina, inda ya ce an kore su ne saboda wasu munanan ayyukan da suka shafi jam’iyyar, ciki har da amincewa da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, Dakta Dikko Radda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Basaraken Gargajiya Ya Fadi,Ya Rasu A Fadarsa
“Kamar yadda kuka riga kuka sani, wani sashe na shugabannin zartaswar jam’iyyar na jihar ya kira wani taro ba tare da izini ba a ranar Alhamis 9 ga watan Maris, matakin da ya kusa girgiza jam’iyyar.
“An gabatar da taron gaggawa da ya kunshi mambobi 19 cikin 29 domin tattauna musabbabin faruwar haramtacciyar taron.
“Gaskiya sun bayyana cewa an yi taron ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da amincewar kwamitin zartarwa na jiha ba.
“An kuma gano cewa ko da aka aika takardar gayyata taron ba bisa ka’ida ba ga ’yan kwamitin zartaswa na jiha da na kananan hukumomi da masu unguwanni, an sanar da su cewa makasudin taron shi ne tattaunawa da fitar da kudade domin sasanta wasu masu gudanarwa.
“Duk da haka, a taron da aka yi ba bisa ka’ida ba, an shigar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, inda shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Liti, mataimakin gwamnan jam’iyyar, Rabe-Darma, da sauran manyan shugabannin jam’iyyar suka halarta kuma suka gabatarwa mambobin da suka halarci taron kudurunsu na masu sauya sheka zuwa APC.
Usman-Kankia ya bayyana cewa, “Kusan nan da nan, sai ga baki daya filin ya koma rudani tare da kururuwar taken inda wasu ke cewa sam basu amince da wannan kuduri ba”
Kakakin jam’iyyar NNPP ya nuna cewa a ranar 5 ga watan Maris ne jam’iyyar ta gargadi mambobinta, jami’anta, da ‘yan takara kan kulla kawance da kowace da wata jam’iyyar siyasa.
“Saboda haka, jami’an jam’iyya da ‘yan takara a kowane mataki ba su da ikon tattaunawa, ko kulla wata kawance da kowace jam’iyyar siyasa da nufin samun nasara a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisa masu zuwa.
“Duk wanda ya amince da dan takarar wata jam’iyyar siyasa za a hukunta shi kamar yadda kundin tsarin gudanarwar NNPP ya tanada, tun daga dakatarwa zuwa kora.
“Taron namu na gaggawa ya yi nazari tare da yanke shawarar korar jami’ai da mambobin da ke da ruwa da tsaki a wannan taron ba bisa ka’ida ba, bayan amincewar kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa.
Wadanda aka kora din “Su ne Alhaji Sani Liti, shugaban Jam’iyar na jiha, Umar Jibril, sakataren jiha, Mustapha Basheer, shugaban matasa, Dauda Kurfi, shugaban jam’iyar a shiyyar Katsina, Abdulhadi Mai-Dawa, shugabanta a shiyyar Funtua, Dr Sale Mashi, shugaban NNPP A shiyyar Daura, mataimakin Rabe-Darma. Dan takarar gwamna Audu Yandoma,” inji shi.
A wani labarin kuma, NDIC Ta Bayyana Hanyoyin Kare Abokan huldar Bankuna Daga Masu Zamba
Hukumar inshorar ajiya ta Najeriya NDIC ta gargadi abokan huldar bankuna da sauran jama’a da su guji nuna bayanan bankunan su inda ta ce masu damfara suna kara yin kirkire-kirkire.
Hukumar NDIC a cikin gidan yanar gizon ta ranar Juma’a ta ba da shawarwari hudu ga abokan cinikin banki don kiyaye asusunsu daga ‘yan damfara.