Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori ‘yan sanda akalla 18 bisa samun su laifuka daban-daban da suka hada da cin zarafi da rashin da’a da kuma karbar kudi,Punch ta rawaito.
Wannan bisa ga nazarin rahotannin kafofin watsa labaru da ke nuna adadin ‘yan sandan da aka kora a watan Oktoba da Disambar shekarar 2022, da Afrilu, 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Neman Afuwar Duk Wanda Na Batawa Rai — Buhari
A ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 2022, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kori wasu manyan jami’an ‘yan sanda bakwai bisa zargin aikata rashin da’a tare da amincewa da ragewa wasu jami’ai 10 karin girma.
Hukumar ta PSC ta ce jami’an da aka kora sun hada da babban Sufuritandan ‘yan sanda, Sufuritanda na ‘yan sanda daya, da mataimakan Sufiritandan ‘yan sanda biyar, Ya kara da cewa SP daya ya yi ritaya ne domin amfanin jama’a.
Hukumar ta kuma rage darajar CSP zuwa SP, SP uku zuwa DSP; DSP guda biyu zuwa ASPs, da ASP hudu zuwa Insifakta.
A ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2022, kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Muhammed Berde, ya bayyana cewa rundunarsa ta kori ‘yan sanda bakwai bisa samun su da cin mutuncin aikin ‘yan sanda.
Hukumar NPF a ranar 13 ga watan Afrilu, 2023, ta kori wasu manyan ‘yan sanda uku bisa laifin amfani da makami, cin zarafi, rashin da’a da kuma almubazzaranci da harsasai.
Jami’an – Insifekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da Isah Danladi – wadanda ke tare da wani mawakin Kano ne a yayin da masu rakiyar suka dauki hoton bidiyo suna harbin iska.
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta a ranar 19 ga watan Afrilu, 2023, ta kori Insifekta Ubi Ebri bisa zargin kashe wani matashi dan shekara 26, Onyeka Ibe, a hanyar Ugbolu-Illah a garin Asaba bisa zarginsa da kin bayar da cin hancin N100.
A halin da ake ciki kuma, wani lauya mai kare hakkin bil’adama mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi, ya yabawa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, kan yadda ya kiyaye da’a a rundunar.
Olajengbesi, wanda shi ne Manajan Abokan Hulɗa a Law Corridor, ya ce idan aka ci gaba da ɗorawa da kuzari da ƙima na ƙwararru da tsattsauran ladabtarwa, ‘yan sanda za su ga gagarumin sauyi wanda zai rage yawan kashe-kashen da ‘yan sanda ke yi ba tare da shari’a ba.
Ya kara da cewa, “IG Usman Alkali Baba a ‘yan kwanakin nan ya fito karara ya nuna hazakar shugabanci da sanin ya kamata ta hanyar tabbatar da an gurfanar da jami’an da suka aikata laifi ba bisa ka’ida ba.
“Mun shaida yadda ake korar jami’an da suka aikata miyagun laifuka da, rage musu girma da kuma gurfanar da su gaban kuliya, tun daga karbar kudade da zalunci da kashe-kashe ba gaira ba dalili.
“Irin wadannan ayyukan na IG ko shakka babu za su aike da sako mai karfi ga sauran jami’an da za su yi tunanin irin wannan aika-aikar cewa ba za a kara amincewa da irin wadannan halaye a cikin ‘yan sanda ba. Hakanan abin yabo shine fifikon tsawaita ayyukan ladabtarwa a kan kwamandojin tare da ayyukan sa ido kai tsaye akan sanannuwan ‘yan sanda.”
A wani labarin kuma, Shugabancin Majalisar Dattawa Na 10: Dalilin Da Ya Sa Muke Bukatar Adawa – Lawan
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce tilas ne jam’iyyar APC mai mulki ta sanya jam’iyyun adawa a cikin shugabanci domin samar da zaman lafiya a majalisar a daidai lokacin da takarar neman cike manyan mukamai a majalisar dokokin kasar ke kara kamari.
Ya bayyana haka ne a yau Juma’a a lokacin da yake gabatar da amsar tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ya hadu da mazauna babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da bikin Sallah ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Comments 1