Wata matashiyar budurwa ta bayar da mamaki matuƙa a manhajar TikTok, da irin salon tuƙin ta.
A wani bidiyo da ta sanya a shafinta na TikTok mai suna Omoladegold301, an nuna budurwar tana tuƙa babbar motaa yayin da ta ke ta sarrafa sitiyarin motar cikin ƙwarewa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Shugabancin Majalisar Dattawa Na 10: Dalilin Da Ya Sa Muke Bukatar Adawa – Lawan
Bidiyon ya nuna matashiyar budurwar cikin babbar motar tana ta tuƙin cikin ƙwarewa yayin da ta ke ta kewaya wa a cikin wani fili.
Abin ya bayar da mamaki a ce matashiyar budurwa tana sarrafa mota mai girma irin wannan, amma ta nuna cewa komai mai yiwu wa ne idan sanya juriya da mayar da kai.
Mutane da yawa sun yaba mata bisa wannan namijin ƙoƙarin da ta yi, inda suke cewa lallai ta nuna tsantsar jarumta.
Bidiyon ya yaɗu sosai inda ya samu ‘likes’ sama da dubu ashirin da shida (26,000), sannan sama da mutum dubu biyu (2,000) suka yaɗa shi.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon Wata Kyakkyawar Soja Ya Dauki Hankula Sosai
Wani ƙayataccen bidiyo na wata kyakkyawar soja wanda ya nuna tsananin kyawunta a cikin khakin ta na soja, ya ɗauki hankulan mutane sosai.
Sojan tana da wata baiwa ta musamman ta jan hankali kamar yadda ta yi a cikin ɗan gajeran bidiyon wanda ya karaɗe manhajar TikTok.