Wata kotu mai daraja ta daya da ke Kubwa, Abuja, babban birnin tarayya, Abuja, ta tsinke auren shekara 18 na wata mata mai suna Hafizar Saidu da mijinta, Aminu Usman suka yi, sakamakon rashin kula da ita yadda ya kamata.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito, alkalin kotun, Malam Yahaya Sheshi ya raba auren nasu ne biyo bayan rokon da Hafizar ta yi wa kotun na raba aure a bisa dalilin rashin kulawa da cutar da ita da batir.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin Imani: Mijina Yana Lakadamun Dukan Tsiya dani Da Mahaifina — Mata Aure
Sheshi ya umurci Hafizer da ta kiyaye “Iddah” wanda itace lokacin jira da za’a yi na tsawon watanni uku kafin a daura wani sabon aure.
Tun da farko, Hafizer ta shaida wa kotun cewa ta auri Aminu ne bisa tsarin shari’ar Musulunci, kuma aurensu Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyar.
“Usman ba ya kula da ni ko iyalanmu, Yana dukana yana zargina da kuskure.
“Ya je wurin iyayena, ya yi musu duka kuma ya yi barazanar kashe iyayena.
Ta ce: “Cin zarafin da mijina yake ya isa haka kuma ina son a raba aurenmu.
Sai dai wanda ake kara ya musanta zargin da ake masa, amma ya amince a raba auren.
“Idan ban sake ta ba, rayuwata na cikin hadari, idan ban sake ta ba ya mai maita.
“Yan uwanta sun lakada min duka kuma an garzaya da ni asibiti domin a yi min magani.
“Ina rokon wannan kotu mai albarka ta biya mata bukatar ta,” in ji Aminu.
A wani labarin kuma, NPF Ta Kori Jami’an ‘Yan Sanda 18
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori ‘yan sanda akalla 18 bisa samun su laifuka daban-daban da suka hada da cin zarafi da rashin da’a da kuma karbar kudi.
Wannan bisa ga nazarin rahotannin kafofin watsa labaru da ke nuna adadin ‘yan sandan da aka kora a watan Oktoba da Disambar shekarar 2022, da Afrilu, 2023.
A ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 2022, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kori wasu manyan jami’an ‘yan sanda bakwai bisa zargin aikata rashin da’a tare da amincewa da ragewa wasu jami’ai 10 karin girma.
Hukumar ta PSC ta ce jami’an da aka kora sun hada da babban Sufuritandan ‘yan sanda, Sufuritanda na ‘yan sanda daya, da mataimakan Sufiritandan ‘yan sanda biyar, Ya kara da cewa SP daya ya yi ritaya ne domin amfanin jama’a.
Comments 2