Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) ta bayyana gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan da ya fi kowanne gwamna ta fuskar sanya ido kan kula da harkokin kananan hukumomi tare da ba shi lambar yabo.
Da yake bayar da lambar yabo yayin ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a daren ranar Talata, shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Ambali Akeem Olatunji ya ce, “Mun baka wannan lambar yabon ne a matsayinka na uba ga ma’aikatan kananan hukumomi a kasar nan.”
DUBA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Yan Bindiga sun sace tsohon babban Manajan Hukumar NPA
A yayin gabatar da jawabi a otal din Green Desert, dake Kano, a ranar Laraba, lokacin da gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, shugaban kungiyar ya jaddada cewa, “Muna baiwa gwamnan wannan lambar yabo ne saboda irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kananan hukumominmu guda 44.”

Olatunji wanda ya yabawa Gwamna Ganduje bisa kyawawan manufofinsa ga ƙananan hukumomi, kasancewar sa tsohon sakataren karamar hukuma, kuma tsohon shugaban karamar hukuma, wanda hakan ya sanya Olatunji cewa, “Idan kana son zama dan siyasa mai nasara sai a fara tun daga matakin kasa wato karamar hukuma.”
A nasa jawabin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta bakin Mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a wajen bikin bude taron kungiyar na majalisar zartarwar su ta kasa (NULGE), Gwamna Ganduje ya yaba da cewa, “Da farko ina mika godiya ta a madadin gwamnati da kuma na kasa baki daya, da Jama’ar jihar Kano ga wannan kungiya bisa zabar jihar Kano domin gudanar da taron majalisar zartarwa ta na kasa.
Gwamnan ya bayyana cewa ƙungiyar tayi la’akari ne da zaman lafiya da jihar ke da shi, wanda ya basu kwarin gwiwar zabar Kano domin gudanar da taron su.