By Ishaq Dabai
Mutane ukun da suka rage a Hannun masu garkuwa jami’an tsaron jihar Ondo sun kubutar dasu, a cewar rundunar Amotekun, andai farmaki matafiyan akan hanyar Legas a garin Ifira-Akoko dake karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas a jihar lokacin da suka hadu da masu garkuwa da kuma yan fashi.
Hadarin ya farune a marabar titin Idoani-Ifira dake karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas, inda rundunar soji ta Amotekun tabi bayan masu garkuwar inda ta sami nasarar kubutar da mutane tara a ranar alhamis.
Kwamandan na Amotekun, Adetunji Adeleye shine ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya a birnin Akure inda yace sun sami nasarar kubutar da sauran mutane ukun da suke hannun masu garkuwa.
Ya kara da cewa dureban motar ya samu nasarar tserewa bayan da ya dirge daga cikin motar tun ranar da a bin yafaru a marabar titin na Ifira-Akoko.
Inda ya bayyana sunayen wadanda aka kubutar akwai Benjamin Ojoga, da Omolara Fajana da kuma Faith Sunday inda tuni aka mikasu ga iyayensu a hedkwatal rundunar ta Amotekun dake birnin Akure na jihar Ondo.
Masu Garkuwar dai sun farmaki matafiyan a ranar laraba inda suka yi garkuwa da mutane 13 akan hanyar su ta zuwa Legas.
Comments 1