A jiya ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Abuja zuwa Landan domin gabatar da lacca a yau a Kwalejin King.
Lakcar wani bangare ce a bikin Makon Afirka na shekara ta 2023 da makarantar ke yi.
KU KARANTA: Mun Saki Biliyoyin Naira Domin Bankuna Su Wadata Yan Kasa – CBN
Mai magana da yawun sa, Laolu Akande, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce a matsayinsa na shugaban siyasa daga Afirka, laccar Osinbajo za ta mayar da hankali ne kan tambayar yadda Afirka za ta ci gaba a duniya mai cike da sarkakiya.
Ya ce mataimakin shugaban da aka gayyata zai kasance babban bako na King’s College Africa Leadership Centre (ALC) kuma zai gana da manyan jami’an wannan babbar cibiyar gabanin laccar tasa.
Makon Kwaleji na Afirka 2023, “Canza Afirka a Tsarin Duniya Mai Sauyaw.”
“King College London wanda Sarki George IV da Duke na Wellington suka kafa a 1829 ta zama ɗaya daga cikin manyan kwalejoji biyu na Jami’ar London lokacin da aka kafa jami’ar daga baya a 1836.
Makon Afirka bikin ne na shekara-shekara na bincike, ilimi da kuma ayyukan wayar da kan Afirka.
Yana tattaro masana, masu bincike da dalibai suna ba da damar jin ta bakin masana, shugabanni da masu tunani na Afirka.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo nan gaba a cikin makon nan.
A wani labarin kuma: Zaben Gwamna: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 79 Da Ake Zargi Da Karya Doka A Sokoto
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto a ranar Lahadin da ta gabata ta ce jami’an tsaro sun kama mutane 79 da ake zargi da hannu a wasu laifuka a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Wata sanarwa da DSP Sanusi Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan ya raba wa manema labarai a Sokoto, ta ce wadanda aka kama mutane ne da suka saba wa dokar takaita zirga-zirga da kuma wasu laifuka da suka saba wa dokar zabe.