Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya isa birnin Landan domin halartar jana’izar marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth ll.
Farfesa Osinbajo wanda ya bar Abuja ranar Asabar din nan zai wakilci Najeriya a wasu taruka da dama yayin da yake kasar Birtaniya, ciki har da taron jana’izar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Yayin da ya isa Landan ranar Lahadin nan, a cewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Laolu Akande, mataimakin shugaban kasar ya kai ziyarar ban girma a fadar sarauniya ta Westminster.
Ya kuma sanya hannu kan rajistar ta’aziyyar, inda ya ce, “Najeriya ta bi sahun gwamnati, da jama’ar Birtaniya, da kasashe rain9n Ingila, da sauran kasashen duniya wajen mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan gidan sarautar bisa rasuwar sarauniya.”
KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Zai Wakilci Najeriya A Wajen Jana’izar Sarauniya Elizabeth
Bayan haka, Akande a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Farfesa Osinbajo ya samu tarba daga sakataren harkokin wajen Birtaniya, James Cleverly.
A wajen taron, Cleverly ya nuna jin dadinsa ga yadda Najeriya ke marawa kasar Birtaniya baya a lokacin da take cikin bakin ciki, kuma dukkanin mutanen biyu sun tattauna kan sha’awar firaministan Birtaniya, Liz Truss, na kara dankon zumunci da Najeriya.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Daga baya a maraicen (ranar Lahadin), za a karbi Mataimakin Shugaban kasa tare da shugabannin duniya – ciki har da membobin kasashe rainon Ingila, Shugabannin Kasashe, manyan Gwamnoni, Fira Minista, da dangin sarauta na kasashen waje – ta Sarki Charles III da Sarauniya Consort Camilla. a wata liyafa a fadar Buckingham.
Akande ya ce Farfesa Osinbajo zai kuma hadu da ‘yan gidan sarauta da kuma shugabannin duniya a taron jana’izar da aka shirya gudanarwa a Westminster Abbey ranar Litinin.
A wani labarin kuma: Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalinsu A Jigawa Ya Karu Zuwa Mutum 90
Kusan mutane 29 ne suka kara rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa yayin da ruwa ke ci gaba da mamaye al’umma a sassan jihar.
Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu a irin wannan yanayi zuwa 92, in ji hukumomin ‘yan sanda a jihar da ke arewa maso yammacin kasar.