Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan baranda sun ziyarci Ede mahaifar gwamnan jihar Osun Sanata Ademola Adeleke inda suka far wa mambobin jam’iyyar PDP a taron mako-mako da suke yi a Unguwar Gidanba Atapara da ke garin ranar Juma’a.
A cewar majiyoyi a wurin taron, ‘yan barandan sun mamaye taron ne da yammacin ranar Juma’a inda suka harbe wata mata ‘yar jam’iyyar mai matsakaicin shekaru, mai suna “Puranga”, Jaridar Tribune Online ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Tashi Tsaye Wajen Yakar Kashe-kashen Da Ake Yi A Kudu Maso Gabas – Buhari Ga Shugabannin Addinai
‘Yan ta’addan dauke da bindigogi, kulake, wukake, adduna da sauran muggan makamai, sun kuma yi awon gaba da wani yaro mai suna Nureni Olobe, daya daga cikin hadiman shugaban marasa rinjaye da ke wakiltar garin a majalisar dokokin jihar, Honorabul Akogun Kofoworola.
An kuma tattaro cewa ‘yan barandan, a yayin harin, sun kuma kona gidan mahaifin Akogun da kuma na abokansa a garin.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Da yake magana kan lamarin, dan majalisar ya ce: “Wasu ‘yan daba dauke da makamai sun kai mana hari a wani taron unguwanni na jam’iyyar PDP a Ede a ranar Juma’a.”
“Bayan haka na tafi Osogbo, daga baya, an gaya mini cewa suna kai hari gidan iyayena. Sun kona gidan tun a lokacin ban ga mahaifina ba.”
“Ba mu san ko an kashe mahaifina ba ko kuma sun yi garkuwa da shi saboda har yanzu baya nan.”
Sai dai a martaninsa kan lamarin, zababben gwamnan, Sanata Adeleke ya zargi gwamna mai ci, Gboyega Oyetola da shirya makarkashiyar tada zaune tsaye a jihar gabanin ficewar sa daga ofis a watan Nuwamba mai zuwa.
Adeleke, wanda ya yi zargin cewa ajandar Oyetola ita ce ta fara rikici da kuma daukar fansa a Ede domin a karshe ya mamaye jihar gaba daya gabanin gudanar da aikin mika mulki.
Ya ce: “Ina kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukar mataki tare da hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan hari da aka kai wa wani babban jami’in da ba shi da laifi. dan kasa, wanda laifinsa daya ne watakila dansa shine shugaban marasa rinjaye na PDP a majalisar dokokin jihar Osun. Dole ne a daina tashin hankali tunda zabe ba yaki bane.”