By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Adegboyega Oyetola na jihar Osun ya nuna alhininsa bisa rasuwar tsohon shugaban mulkin soja na jihar, Kanar Anthony Uzoma Obi (mai ritaya), inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin mai raɗaɗi.
Obi wanda ya rike mukamin gwamnan mulkin soja na jihar Osun tsakanin watan Agustan shekarar 1996 zuwa Agusta 1998, ya rasu ne a ranar Asabar 1 ga watan Janairu kamar yadda iyalansa suka sanar.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismail Omipidan, Gwamna Oyetola ya jajanta wa iyalan marigayin tare da yabawa gudunmawar da ya bayar wajen gudanar da mulki a Osun, inda ya ce yana daya daga cikin shugabannin da suka aza harsashin ginin jihar.
Sannan ya ce, “Mutuwar Kanar Anthony Obi (mai ritaya) abu ne mai raɗaɗi kuma babban rashi ne ba ga danginsa kaɗai ba har ma ga ƙasa baki daya. Wanda ya kasance Jajirtacce ne, kuma gogaggen hafsan soja wanda ya yi wa Nijeriya hidima da kuma jihar sa ta Osun musamman sadaukar da kai da kishin kasar daya nuna.
“A matsayinsa na jami’in soja, Obi ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen gudanar da mulki a jihar Osun, kuma yana daya daga cikin shugabannin da suka kafa harsashin ginin Jiharmu kuma ya bar wasu abubuwan gado da za a rika tunawa da shi.
“A madadin iyalaina, gwamnati, da kuma al’ummar Osun, ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalan Kanar Anthony Obi (mai ritaya).Ko da yake mutuwarsa tana da ban tsoro, ina roƙon ku da ku yi ta’aziyya a gadon rashin son kai, ƙwarewa, da hidima ga bil’adama daya bari.”
Gwamna Oyetola ya yi addu’ar Allah ya jikan mamacin ya kuma baiwa ‘yan uwa da abokan arziki hakurin jure wannan babban rashi.