PDP Ba Za Ta Yarda da Kuri’un da suka fito daga Wuraren da ba za’a Iya Shiga Ba —Ayu Ya Gargadi INEC
Jam’iyyar PDP ta gargadi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cewa ba za ta karbi kuri’u daga wuraren da ba za a iya shiga ba a lokacin gudanar da babban zaben kasar.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da Cibiyar Dimokradiyya (PDI), Asokoro a Abuja ranar Juma’a, Shugaban Jam’iyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya ce ba kamar sauran jam’iyyu ba, PDP na kirga kuri’un ‘yan Nijeriya, inda ya kara da cewa “Za mu ta yi kasa a gwiwa, lokacin da yardar Allah da kuri’un ‘yan Najeriya, PDP za ta dawo mulki a badi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ban shirya dena ƙara girman laɓɓa na ba, Matar da tafi kowa girman leɓe a duniya
“Dole ne mu mayar da hankali a kan mu dawo da mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a watan Fabrairu mai zuwa domin mu fara aikin dawo da da ya lalace daga shekarar 2015.
“PDP tana kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawarinsa na tabbatar da cewa zaben 2023 ya kasance cikin ‘yanci, gaskiya, da Adalci. Fadar shugaban kasa da APC kada su tsoratar da INEC ko jami’anta ta kowace hanya: kowace kuri’a ta kirga.”
“Ba za mu amince da girbin kuri’un da aka samu daga wuraren da ba za a iya kaiwa ba kamar yadda ya faru a zabukan da suka gabata a karkashin jam’iyyar APC.”
Shugaban ya kuma yi kira ga kasashen duniya, “musamman kasashen Amurka, Tarayyar Turai, Commonwealth da Tarayyar Afirka da su ci gaba da sha’awar aikin dimokuradiyya a Najeriya ta hanyar matsin lamba na diflomasiyya, huldar siyasa da manyan tawaga masu sa ido.”
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kaddamar da zaben, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yabawa Ayu da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde kan sake farfado da dimokuraɗiyya.
Ya ce an kafa PDI ne domin inganta bincike, horarwa da sauran abubuwan ci gaban dan Adam na jam’iyyarmu. “Wannan cibiya za ta gudanar da abubuwa da dama tun daga bincike zuwa horo zuwa kara kuzari da dai sauransu.
“Bari in yaba wa duk wanda ke da hannu wajen farfado da wannan cibiya, ina so in tabbatar muku, idan muka sake samun damar zaben mutanen Najeriya za mu tabbatar da cewa an samar da wani gini na dindindin ga PDI.
A wani labarin kuma: Ban shirya dena ƙara girman laɓɓa na ba, Matar da tafi kowa girman leɓe a duniya
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da duk wasu kudaden da jihohin Neja Delta ke karba tun 1999.
Wike ya bayyana cewa, an yi amfani da wani bangare na kudaden ne wajen ayyuka da dama da gwamnatinsa ta gina.