Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Haliru Bello Muhammed, ya ɗora laifin cigaba da nuna yatsa tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas kan gazawar kwamitin amintattu BoT na ɗaukar mataki da wuri.
A ranar Jumu’a, wakilan Atiku karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa suka gana da tawagar gwamna Wike a Patakwal, babban birnin Ribas, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dimokuraɗiyya ta fahinci cewa ɓangarorin biyu sun zauna da juna ne da nufin lalubo hanyar sasanta jiga-jigan guda biyu.
Yayin wata hira da kafar talabijin ta Channels TV cikin shirin ‘Siyasa a yau,’ Muhammed ya ce ya kamata BoT su yi hanzarin rarrashin Wike.
A kalamansa ya ce, “An tafka kuskure a ɓangaren BoT, kwamitin ke da hakkin shiga tsakani da warware batutuwa da suka shiga tsakanin mambobin jam’iyya, ko tsakanin jam’iyya da majalisa, ko tsakanin majalisa da shugaban ƙasa idan mu ke kan madafun iko.”
KANTA ANAN: Mun Ruguza Jam’iyyun Adawa A Jihar Ribas – Wike
“Amma tun da bamu ke da shugaban ƙasa ba, BoT ba su yi abin da ya kamata ba, da ace BoT sun shigo sun tsawatar wa jam’iyya da wannan matsalar ba ta lalace haka ba, amma duk da haka bamu makara ba. Jam’iyya ta tsara wasu matakai kuma muna aiki baji ba gani kan matsalar, ina da yakinin bayan taron Patakwal, ba za’a sake jin wata matsala ba.”
“Gwamna Wike zai dawo ya haɗu da yan uwansa maza da mata jagororin jam’iyya daga nan mu tunkari gaba domin lashe zaɓen 2023 da ke tafe.”
A wani labarin kuma, Tawagar Atiku Abubakar ta gana da gwamna Wike a Patakwal
Tawagar Atiku Abubakar ta gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal ranar Juma’ar nan.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, An gudanar da taron ne a sirri a gidan Wike na musamman.