Wata babbar kotun tarayya da ke zama a babban birnin tarayya Abuja, ta yi watsi da karar da Hon. Sani Idris Kutigi ya shigar kan Hon. Isah Liman Kantigi, wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Neja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Sadarwa na kwamitin Yakin neman zaben PDP na Jihar Neja, Usman Mohammad Yahaya da mai taimaka wa kan harkokin yada labarai, Comrade Israel kolo, a Minna.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Najeriya Miliyan 133 Ne Ke Rayuwa A Cikin Talauci – FG
A cewar sanarwar, wanda ya sha kaye a hannun Kantigi, ya shigar da karar yana neman a soke Kantigi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 a kotun tarayya da ke Abuja.
A cewar sanarwar: “Shugaban alkalin kotun, Hon. Mai shari’a Zaynab Mohammed ta ce Hon. Sani Idris Kutigi ba shi da wani dalili na daukar mataki don haka, saboda haka, an “kori karar.”
Kantigi ya doke wasu ’yan takara hudu inda suka samu tikitin takarar jam’iyyar a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 26 ga watan Mayu, 2022. Wadanda suka yi takarar sun hada da Sani Idris Kutigi, Sidi Abdul Gulu, Barista Abdulrahman Gimba da Engr Abubakar Isah Jankara.
Kantigi ya samu kuri’u 667 daga cikin kuri’u 808 inda ya zama wanda ya lashe zaben, yayin da abokin hamayyarsa Sani Idris Kutigi ya samu kuri’u 114. Isah Jankara da Gimbal Abdul Rahman sun samu kuri’u 21 da kuri’u 3 yayin da Alh Sidi Abdul bai samu ko kuri’a ba.
A WANI LABARIN KUMA: 2023: PDP Tace tana da tabbacin Lashe Jihar Lagos da wasu Jihohi 24
Jam’iyyar PDP ta sha alwashin lashe jihohi 25 ciki har da jihar Legas a babban zaben shekara mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyana haka a wani taro a Abuja domin karbar rahoton kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP na jihar Legas da Osun.
“PDP za ta samu gwamna a Legas da wasu mukamai da dama a majalisar dattawa, da wakilai, da na majalisu Dokoki na Jihohi,” in ji Ayu.