By Abbas Yakubu Yaura
Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya amince da gudanar da taron jam’iyyar shiyyar Arewa maso Yamma na zaben shugabannin shiyyar da kuma tsohon ofishi na kasa a shiyyar Arewa maso yamma.
Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Asabar ya bayyana cewa an shirya gudanar da atisayen ne a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, 2022, a hedikwatar shiyyar Kaduna dake jihar Kaduna.
Imo: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar Da Hallaka ‘Yan Bindigar Da Suke Da Hannu A Mutuwar Jami’in Ta
Kwamitin Jam’iyyar adawa NWC ya bukaci dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da kuma jiga-jigan mambobinta a yankin Arewa maso Yamma da su jagorance su don gudanar da atisaye ba tare da samun wata matsala ba.
PDP ta ba da tabbacin cewa za a gudanar da taron na shiyyar Arewa maso Yamma bisa ga kundin tsarin mulki da ka’idojin jam’iyyar, da kuma bin ka’idar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) kan COVID-19.
Wannan dai na zuwa ne bayan wa’adin da hukumar zabe mai zaman kata ta kasa INEC tayi inda ta gargadi jam’yyun siyasa dasu gudanar da taruka da zaben fidda gwani kafin karshen wannan watan da muke ciki na Mayu.
Hukumar ta INEC a ranar 5 ga watan da muke ciki na Mayu 2022 taja kunnen jam’iyyu cewa zasu iya fuskantar rashin cancanta muddin suka kasa cika umanin data gidan daya na kammala zaben fidda gwani da wasu ayyukan masu alaka da hakan.
Comments 1