Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe, a ranar Lahadi, ta gargadi tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Adamu Waziri, bisa zarginsa da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a jihar, ta hanyar daukar nauyin wata zanga-zangar nuna adawa da tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo.
Jam’iyyar ta sake tabbatar da biyayyar ta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 mai gabatowa, Atiku Abubakar, tare da bayyana shugabancin Dankwambo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Ƙano Ta Sha Alwashin Hukunta Masu Ɓarnata Kayan Gwamnati
A cewar sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na jihar Gombe, Murtala Usman, yayin da yake mayar da martani kan zanga-zangar da wasu matasa da ake zargin Waziri ne ya dauki nauyin yi, wadanda suka mamaye sakatariyar jam’iyyar ta jihar suna zanga-zangar nuna adawa da Ibrahim Dankwambo, ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa.
Usman ya ci gaba da cewa, “A yau ne wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP daga jihar Yobe suka kai wa ofishin jam’iyyar PDP hari domin yi wa shugaban jam’iyyar mu Ibrahim Hassan Dankwambo (Talban Gombe) bore tare da nuna bakin jini da haddasa rashin jituwa da hargitsi a cikin jam’iyyar a jihar Gombe.”
“Mai daukar nauyin wanda ya tsaya takara sau da yawa a jihar Yobe kuma bai iya lashe ko daya ba, sanannen dan takara ne kuma dan kasuwar siyasa.”
“Ya kamata ya je ya damu kansa da rikicin siyasar da ke addabar jihar Yobe, ya daina tsoma baki cikin harkokin siyasar jihar Gombe.”
A yayin da take jaddada goyon baya ga Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa, jam’iyyar ta lura cewa Dankwambo a matsayin shugaba ba zai girgiza ba, tana mai jaddada cewa burin jam’iyyar ya kasance na lashe zaben shugaban kasa da na gwamnoni a jihar.”
“Shugabannin jam’iyyar a jihar Gombe suna biyayya dari bisa dari ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa). Muna kuma so mu bayyana wa dukkan magoya bayanmu cewa mun yi imani kwata-kwata da shugabancin Ibrahim Hassan Dankwambo (Tolban Gombe) a matsayin shugaban jam’iyyarmu kuma babban mai goyon bayan PDP daga sama har kasa. Alkawarinmu shi ne lashe zaben 2023 a dukkan matakai a jam’iyya,” Usman ya kara da cewa.
A wani labarin kuma, Atiku Ya Fi Cancanta Ya Zama Zabin Yan Najeriya a 2023, Saraki
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi shiru kan rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Saraki wanda ya rufe baki tun bayan rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar 28 ga watan Mayu ya kada shi, a ranar Asabar, ya bayyana cewa ya tafi hutu.