Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni Ya tarbi Hajiya Musafaram tsohuwar jagora a Jam’iyar PDP da ta sauya sheka daga jam’iyar zuwa APC mai mulki a Jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Daraktan Janar na yada labarai da kula da harkokin kafafen yada labaran Gwamnan Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan acikin wata sanarwa da ya fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa: Sarkin Musulmi Ya Fadawa Yan Najeriya Mafita
Ta sanarwar ta bayyana cewa, Hajiya Musafaram wacce jigoce a Jam’iyar PDP, wacce ta dade a jam’iyar tun a shekarar 1999 ta dawo Jam’iyar APC Mai Mulki
Da take jawabi, Hajiya ta bayyana cewa, Ayyukan Gwamnatin Bunina bunkasa rayuwar al’ummar jihar ne ya sanyata ta sauya sheka zuwa APC .
Kazaljka Gwamna Buni ya kuma tarbi tsohon Mamba a Majalissar Zartaswa ta Jam’iyar PDP a Karamar hukumar Geidam zuwa jam’iyar APC mai mulki.
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Gwamnan ya tabbatarwa Sabbin Mambobin Jam’iyar APCn cewa, za su sami dama kamar yadda Sauran ya’yan jam’iyar APCn suke samu.
A WANI LABARIN KUMA: Lawan Ya Sake Shan Kaye, Kotu Ta Tabbatar Da Machina A Matsayin Dan Takarar APC
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar kan dantalarar Sanatan Yobe ta Arewa.
Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensen, wadda ta jagoranci wani kwamiti mai mutane 3, tabbtar da hukunci bayan da ta saurari mahawara daga bangarorin biyu da lamarin ya shafa