Jam’iyyar PDP tayi Allah wadai da harin ƴan bindiga a ranar Talata a Jami’ar Abuja, wanda suka sace ma’aikata 4 da wasu ƴaƴan su.
Jam’iyyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaru na Jam’iyyar Kola Ologbondiyan a ranar Talata a Abuja, inda ya bayyana harin a matsayin ‘abin mamaki’.
Jam’iyyar ta buƙaci ayi gaggawar sakin waɗanda lamarin ya shafa, gami da haɗa su da iyalan su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Lagos zata biya kuɗin maganin waɗanda aka ceto a ruftawar ginin Ikoyi
PDP ta shawarci Shugaba Buhari a matsayin alƙawarin daya sha, daya bada umarni na ganin an ceto wanda lamarin ya rutsa dasu.
Jam’iyyar tayi kira ga Jami’an tsaro da kada su gajiya, wajen gano ƴan bindigar tare da ceto lamarin ya shafa.
Ta kuma bayyana yawaitar matsalolin tsaro a ƙasar, tare da yin kira ga ƴan ƙasa dasu taimakawa jami’an tsaro wajen ƙoƙarin samar da tsaro a ƙasar.
“Jam’iyyar PDP tayi kira ga ƴan Najeriya dasu cigaba da addu’ar samun nasara da lafiyar wanda aka sacen, tana mai kira ga jam’iyyar dasu ƙara azama wajen samar da tsaron ƙasa.