Amintattun jam’iyyar PDP sun kafa wata kwamiti da za ta duba matsalolin da ‘ya’yanta suke fama dashi a Kano, Edo da Legas.
Shugaban Amintattun, Sanata Walid Jibrin ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Jumma’a.
Ya ce, kwamitin amintattun ta hada wasu da za su kula da ayyukansu.
“Mun umurcesu da su dau mataki akan matsalolin da suke addabar jam’iyyar, mun lura a akwai korafe-korafe a Edo, Kano, Legas da sauransu.
“Bayan sun binciko matsalolin, za mu yi kokarinmu wajen magancesu kafin shekarar 2020,” inji shi.
Jibrin ya kuma ci gaba da cewa sun umurnci bangaren aikace-aikace na jam’iyyar su hada kwamitin da zai biciki hakikannin abin da ya faru a zabukan Kogi da Bayelsa.
“Muna jin zarge-zargen da mambobinmu suke yi wa juna a jihohin Kogi da Bayelsa, musamman ma Bayelsa.
“Yanzu dai ba zamu yi gaggawan daukar hukunci ba. Sai mun yi bincike mun tabbatar kafin zamu bullo da maganin matsalar.
“Shi yasa muka umurci Kwamitin aikace-aikacen jam’iyyar su dauki binciken da muhimmanci,” inji shi.