Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, yana mai cewa ba zai iya lashe zaben shugaban kasa da ke tafe ba. Kammar yadda Daily Post ta ruwaito.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriyan ya koka da yadda aka rika kai masa hare-hare da tsangwama biyo bayan furucin da ya yi game da Obi ke da shi, a lokacin da yake Gwamna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: NBC Ta Ci Tarar Arise TV Kan Rahoton Zargin Tinubu
A wata doguwar sanarwa da Gwamna Soludo ya fitar, ya yi zargin cewa Obi yana wasa ne kawai.
Wani ɓangare na bayanin nasa ya nuna cewa, “Bari mu fito fili: Peter Obi ya san cewa ba zai iya ba kuma ba zai yi nasara ba.
“Ya san wasan da yake yi, mu ma mun sani; kuma ya san cewa mun sani.
“Kowa ya san cewa babu inda zai je, amma suna neman wanda za su dorawa alhakin hakan ne kawai.”
Ya kuma kara da cewa mutane biyu ne ko Jam’iya biyu kawai ke da zarafin lashe zaben takarar shugaban kasan.
Da yake yi masa fatan alheri, Soludo ya ce yana addu’ar Obi ko Farfesa Umeadi na APGA guda daga cikin su ya yi nasara.
A WANI LABARIN KUMA: Kotu Ta Sake Soke Zaben Fidda Gwanin Dan Takarar Gwamna Na APC A Jihar Taraba
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta soke zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC da ya tsayar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a yau.
Idan dai za a iya tunawa, tun da fari, babbar kotun tarayya da ke Jalingo a jihar Taraba ta sauke shi daga mukaminsa na dan takarar gwamnan jam’iyyar a babban zabe mai zuwa
Comments 1