Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa ta ci tarar gidan Talbijin Na Arise TV kudin da ya kai Naira Milliyan biyu savoda yada rahoto karya kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC Bola Ahmed Tinubu Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Gidan Talbijin din ya yada wani labari da ke cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na zargin Tinubu da badakalar saffarar miyagun kwayoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Sake Soke Zaben Fidda Gwanin Dan Takarar Gwamna Na APC A Jihar Taraba
Wannan labari na Arise TV ya karade kafafen sada zumunta na zamani amma hukumar ta INEC a ranar asabar ta karyata rahoton ta na mai cewa wannan aikin barna ne
Kazalika a ranar Lahadi gidan Talbijin na Arise TV ya nemi afuwar Bola Tinubu da hukumar zabe mai zaman kanta taka game da labarin karyan da ta yada wanda ya karkatar da hankulan al’umma.
Acewar Jaridar The Nation, an ci tarar gidan Talbijin din tarar naira Milliyan Biyu bisa karya dokar yada labarai.
A WANI LABARIN KUMA: Na Gayyaci Buhari, Obi, Da Kwankwaso, Duk Wanda Cutar Hawan Jini Takamashi Kan Hakan Shi Ya So—- Wike
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya caccaki wadanda ke sukarsa kan ya gayyaci wasu muhimman mutane zuwa kaddamar da ayyukansa a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin da yake kaddamar da Cibiyar Duba lafiyar Zuciya da kuma Gwajegwajen cutar Daji a Fatakwal da akai wa Lakabi da Dr Peter Odili Cardiovascular and Cancer Screening Centre
Comments 1