Gamayyar Kungiyoyin Kwadago ta Nijeriya ta yi Barazanar tsunduma cikin yajin aikin gama-gari muddin hukumomin kasar ba su fara aiwatar da matsayar da aka cimma ba kan biyan albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.
Kungiyar ta TUC, ta sha alwashin kassara harkokin kasar baki daya a ranar 16 ga watannan nan Oktoba idan har ba fara biyan sabon albashin ba.
A baya hukumomin kasar da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya kan wannan albashi, amma bayanai na nuni da cewa, har yanzu ba a fara aiwatar da sabon tsarin ba a mafi akasarin jihohin kasar.
“Yajin da za mu shiga ranar 16 ga watan nan, yajin gama-gari ne, gabaki daya ma’aikatan Nijeriya za mu tabbatar ba su fito aiki ba.” In ji mukaddashin Babban Sakataren kungiyar kwadago ta TUC a Nijeriya, Kwamared Nuhu Toro a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.
Ya kara da cewa, “filayen jiragen sama insha Allahu za mu durkusar da su, wautar lantarki ba za a same ta ba, sannan har Fadar shugaban kasa ba za a samu wutar lantarki ba.”
Su dai ma’aikatan na Nijeriya na so ne a fara biyan Naira 30,000 a matsaryin albashi mafi karanci kamar yadda aka yi yarjejeniya da su da gwamnati.
Gwamnatin shugaba Buharin dai ta ce ta ware sama da Naira biliyan 500 a cikin kasafin kudin badi domin biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar.