Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Ranar 5 ga watan Oktoban ko wacce shekara, rana ce da Hukumar Ilimi, Kimiya da Al’adu ta Duniya (UNESCO) ta ware domin tunawa da gudumawar da Malamai suke bayarwa wajen ciyar da al’uma gaba.
Kamar yadda ake gudunar da bikin wannan rana a suaran sassan Duniya wanda Kasar Nigeria ma tana ciki, Kungiyar Malamai a jihar Yobe itama ba a bar ta a baya ba.
Taron tunawa da wannan rana ya gudana a dakin taro na Kungiyar Malaman Jihar Yobe (NUT) dake kan hanyar Gashua a birnin Damaturu fadar mulkin jihar Yobe.
Da yake gabatar da jawabi a taron, Shugaban Kungiyar Malamai ta kasa Dr. Nasir Idriss wanda Comrade Lawan S. Ibrahim ya wakilta, ya ja hankulan Gwamnatoci daga matakin kasa har zuwa shiyoyi, da suyi amfani da ka’dojin koyarwan da Hukumar Kwadogo ta kasa da kasa (I.L.O) da UNESCO suka bukaci a soma dabbaka su.
Ya kuma yi amfani da wannan dama, wajan yin kira ga Malamai da su kara kaimi wajen bada ilimi mai inganci ga yara domin samun intacciyar al’uma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudin 2022 a ranar Alhamis
Shima da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Malaman na jihar Yobe, Comrade Ado Idriss ya ce, matsalar karancin Malamai a makaruntun jihar ya zamo abun dubawa.
“Sakamakon ritayar da Malamai suke yi, musamman wadan da aka dauke su aiki a shekarun 1980, an samu gibi da yawa yana mai nuna bukatar cewa Gomnati ta dauki sabbin Malamai domin a cike wannan gibin, inji Comrade Idriss.
Ya yabawa Malaman jihar Yobe kan jajircewan da suke yi wajen samar da ilimi, inda yace duk da matsalar tsaro da ya addabi yankin, basu yi kasa a gwuiwa ba.
A jawabin sa, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni wanda Kwamishinan ilimi a matakin farko Dr. Muhammad Sani Idriss ya wakilta, ya ce Gwamnatin sa, tana iyaka kokarin ta wajen bunkasa harkar ilimi.
“Bisa la’akari da muhimmancin ilimi, Gwamnatin nan ta kafa dokar ta baci a bangaren ilimin matakin farko, kuma hakan ya soma haifar da-da mai ido”, in Gwamna Buni.
Ya alkawarta cewa, Gwamnatin sa za ta ci gaba da yin iyaka kokarin ta, domin inganta walwalar malamai a fadin jihar.
Kazalika Taron ya samu halartar manyan jami’ai na bangarorin ilimin jihar daban-daban.
Jim kadan bayan kammala jawabai a taron, Shugaban Kungiyar Malaman na jihar Yobe ya jagoranci wakilin Gwamnan zuwa wajen kaddamar da masaukin baki, motoci da wasu kayayyakin da Kungiyar ta samar.