Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a ranar Asabar, ya saki fursunoni 16 daga gidan yari na kasa dake Ondo.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai shari’a na jihar, kuma kwamishinan shari’a, wanda kuma shi ne shugaban majalisar ba da shawara ta jihar kan jinkai, Mista Charles Titiloye.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Wike, Ortom, Makinde da Wasu Kusoshi Zasu Yi Wa PDP Aiki – Okowa, Wabara
Bayanin hakan ya fito ne ta hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Mista Richard Olabode.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa gwamnan ya kuma sassauta wa wasu daurarru 17 hukuncin zaman gidan yari daban-daban a cibiyoyin da ake tsare da su a jihar.
An lura cewa matakin da gwamnan ya dauka na daga cikin bukukuwan murnar cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Sanarwar ta ce, “Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Akeredolu, SAN. ya umurci Kwanturolan Hukumar Kula da gidan Gyaran hali da tarbiyya na Tarayya a jihar da ya saki fursunoni 16 daga wuraren da suke tsare domin bikin ranar samun ‘yancin kai na bana.”
“Wannan ya yi daidai da ikon da aka bai wa gwamna ta hanyar sakin layi (a) (c) da (d) na karamin sashe na (1) na sashe na 212, na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, 1999 (kamar yadda aka gyara).”
‘Fursunonin da ke zaman gidan yari daban-daban a cibiyoyin sun samu alheri da rahamar gwamnan bisa kyawawan halayensu. Majalisar Ba da Shawarwari ta Jiha ta ba da shawarar a sake su.
“Gwamnan ya bukaci fursunonin da aka saki da su kasance masu halin kirki kuma su dauki sakin su a matsayin wata dama ce a gare su ta yin rayuwa mai inganci ba tare da aikata laifuka ba. Gwamnan ya yi kira ga ‘yan jihar da kada su rika nuna musu wariya, su hada su cikin al’ummominsu daban-daban.”
A wani labarin kuma, Har Yanzu Muna Kan Magana Da Fusatattun ‘Yan Jam’iyyar PDP – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyar PDP ta gane kura-kuran da aka tafka a baya, kuma tana aiki tukuru domin samun daukakar da ta bata.
Atiku wanda ya je Gombe domin halartar bikin aure, ya bude wani ofishin yakin neman zabe a takaice domin tabbatar da burinsa na zama dan kasa lamba daya a 2023.