Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi alkawarin tallafawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci da kuma dakile masu tsattsauran ra’ayi.
Shugaba Putin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan Najeriya a kasar Rasha, Farfesa Abdullahi Y. Shehu, wanda ya mika masa takardar amincewarsa a fadar Kremlin na Gwamnatin kasar.
A game da takamaiman fannonin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da Najeriya, shugaba Putin ya ba da tabbacin fadada kyakkyawar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tabbatar da zaman lafiya, samun daidaito a kasuwannin iskar gas na duniya, yaki da ta’addanci da kuma dakile tsattsauran ra’ayin addini.
Ya ce kasarsa a shirye take wajen yin hadin gwiwa da dukkan kasashe ba tare da togiya ba amma bisa daidaito da mutunta muradun juna, tare da kiyaye ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan juna.
Putin ya bayyana cewa, Rasha a shirye take don mu’amala mai dimbin yawa da kasashen duniya,, domin cin moriyar juna da kasashen da sabbin wakilansu suka zo wakilta a Rasha.