Ministan kwadagon Nijeriya, Dakta Chris Ngige, ya yi gargadin cewa, kasar za ta iya tarwatsewa ba da jimawa ba matukar dai ba a dauki matakai a kan magance matsalar rashin aikin yi a cikin kasar cikin hanzari ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a Enugu a karshen makon nan a wajen da ya amshi lambar girmamawa daga kwalejin lafiya ta Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka tare da wasu manyan mutanen da su ka kamala karatunsu a cikin jami’ar.
Da ya ke yin nazari a kan matsalar yawaitan rashin aikin yi a cikin kasar, Ministan cewa ya yi, idan har wannan matsalar ba a magance ta ba a cikin hanzari, za ta iya kai kasar cikin yamutsi kamar na kasar Benezuela, ya na mai karawa da cewa, yamutsin kuma zai iya shafan kowa.
Ya yi nuni da cewa, alamomin tashin hankali a Nijeriya a bayyane su ke, yana mai cewa, gwamnatin da Shugaba Buhari ke yi wa jagoranci ta dauki wasu matakai na magance matsalar rashin aikin yi din a cikin kasar nan.
“Alamomin suna nan a sarari, Boko Haram alama ce ta rashin aikin yi a Nijeriya. IPOB ma alama ce ta rashin aikin yi. Duk labarin guda a kan ayyukan ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda a shiyyar arewa maso yamma. Hakanan masu yin garkuwa da mutane a duk sassan kasar nan, ayyukan masu lalata bututun mai, OPC – duk wadannan alamomi ne da suka haifu daga cutar rashin aikin yi.
“Ya zama tilas mu dauki dukkanin matakai na yakar matsalar ta rashin aikin yi. In kuwa ba hakan ba da ni da ku manema labarai duk za ta shafi kowa ne.
“Ga alama nan a sarari a lokacin da kake tuka motarka ka shiga cikin cinkoso, sai ka ga wasu suna kwankwasa maka tagar motarka suna neman ka ba su wayarka. In kuma ka hana su su kai maka farmaki.
“Watarana sai sun hana mutane cin abinci a cikin gidajensu. Za su kwankwasa su ce kawo abincin da kake ci, mu ma za mu ci. Ba za mu so abin ya kai ga hakan ba. mun yi kokari a matsayinmu na kasa. Muna kan tafrki guda ne da kasar Benuzuela. Mun yi sa’a Shugaba Buhari ya zo, in kuwa da ba hakan ba, da mun fada tafarki guda da kasar ta Benuzuela. Da duk mun watse zuwa kasashen makwafta.
“Da mun auka a cikin yamutsin da ba za mu iya fitar da kanmu a cikinsa ba. muna kan kokartawa. Muna yin duk abin da muke iyawa domin magance lamarin.
“Hatta a wajen taron majalisar zartarwa ta kasa na baya-bayan nan da aka yi, an nanata cewa duk wata kwangila da za a yi na wasu mahimman ayyuka tilas ne a nuna yawan ayyukan yin da aikin zai samar. Akwai kuma sauran wasu abubuwan da muke yi a matsayinmu na gwamnati domin mu ga yanda za mu magance lamarin.
Kwalejin Lafiyan ta Jami’ar ta karrama wasu daga cikin tsaffin daliban makarantar ne kamar su, Dakta Chris Ngige, Dakta Peter Odili, Sanata Chimaroke Nnamani, Dakta Okwesilieze Nwodo, a bisa gudummawar da suke baiwa makarantar, hakanan shi ma hamshakin dan kasuwan nan na Duniya, Yarima Arthur Eze, da kuma Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, duk kwalejin ta karrama su.