Ƴan Najeriya dake zaune a ƙauyukan dake kusa da iyakokin Najeriya sun koma yin cinikayya da kuɗin Cefa, kuɗin da ake amfani da su a ƙasashe rainon Faransa, yayin da ƙarancin sababbin kuɗaɗe na Naira ke ƙara ƙamari.
A cewar rahoton jaridar Legit.ng manoma da ƴan kasuwa a ƙauyukan Mfum, Gurin da Illella, a jihohin Cross River, Taraba da Sokoto, sun koma amfani da Cefa domin rage raɗaɗin da rashin sababbin kuɗin ya haifar.
KU KARANTA KUMA: Sabon salo: Ɗan achaɓa ya kawo sabuwar hanyar da mutane za su riƙa biyan shi haƙƙin sa
Ƴan kasuwar sun bayyana cewa yin cinikayya da Cefa ba sabon abu bane amma dai ƙarancin sababbin kuɗin ya sanya an samu ƙaruwar yin cinikayya da Cefa a ƙauyukan na iyakokin Najeriya.
A yanzu haka, ƴan kasuwa da manoma a ƙauyukan suna mayar da kayayyakin su a kuɗin Cefa sannan za su mayar da su zuwa kuɗin naira idan an samu wadatuwar ta.
Daga Zuwa Rabon Faɗa, Matar Aure Ta Gandarawa Surikinta Cizo a Mazakuta
A wani labarin na daban kuma, wani tsoho yaga ta kansa bayan surikar sa tayi masa wani ɗanyen aiki
Wani tsoho mai shekara 78 a duniya, wanda ya fito daga gundumar Bumula, a yankin Bungoma na ƙasar Kenya, yana can yana jinya bayan surikarsa ta gandara masa cizo a mazakuta yayin da suka samu saɓani.
Tsohon mai suna Vincent Barasa, matar ɗan sa ta biyu suna is Evelyn Okello, itace tayi masa wannan aika-aikar a ranar 28 ga watan Janairun 2023, yayin da yake ƙoƙarin raba su faɗa da wata ƙawarta a gidan su.