Wata mata wacce ta rabu da mijinta saboda yayi mata kishiya ta ƙare da auran mai mata biyu inda taje a matsayin ta uku.
Wani mai amfani @KawuGarba a Twitter shine ya sanya wannan labarin a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairun 2023.
KU KARANTA KUMA: Mamban kwamitin amintattu na PDP ta kasa ya fice daga jam’iyyar
Matar tayi ɗawainiya da tsohon mijin nata inda itace ta ɗauki nauyin karatun sa a makarantar koyon aikin lauyoyi.
Bayan ɗaukar nauyin karatun na sa, yana samun madafa kawai sai yace sai ya ƙaro aure, hakan ya fusata matar matuƙa.
Ganin ba zata iya ɗaukar wannan abun ba ya sanya ta nemi da ya bata takardar ta.
Mijin yayi iyakar bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ba su rabu ba amma ta tubure tace dole sai ya sallameta.
Bayan ta hura masa wuta ita da ƴan’uwanta, daga ƙarshe ya yarda ya sake ta, amma ya karɓe dukkanin ƴaƴan sa guda uku.
Shekara huɗu bayan rabuwar su, matar yanzu ta ƙare da auren mai mata biyu, hakan ya sanya ta zama mata ta uku a wajensa kenan.
Hakan ya sanya masu sharhi kan labarin a Twitter bayyana mabanbanta ra’ayoyi.
Wani mai sharhi daga ciki yace matar da haƙuri tayi da mijinta na farko da ya fiye mata.
Samari Sun Koya Min Hankali, Cewar Wata Budurwa Mai Ɗauke Da Juna Biyu
A wani labarin na daban kuma wata budurwa ta bayyana yadda ta ɗandana kuɗarta a hannun samari.
Wata budurwa mai ɗauke da juna biyu ta koka kan yadda samari suka wahalar da ita da sunan soyayya a kafafen sada zumunta.
Budurwar a cikin wani bidiyo ta zubar da hawaye yayin da take bayyana cewa ta daina fitowa waje saboda kunyar da take ji
Budurwar ta bayyana hakan ne dai a wani bidiyo da mai amfani da @bethblinky ta sanya a manhajar TikTok.