Wata budurwa mai ɗauke da juna biyu ta koka kan yadda samari suka wahalar da ita da sunan soyayya a kafafen sada zumunta.
Budurwar a cikin wani bidiyo ta zubar da hawaye yayin da take bayyana cewa ta daina fitowa waje saboda kunyar da take ji. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Budurwar da aka kwashewa N4m tayi watsi da bayanin bankin, tace kuɗinta kawai ta sani
Budurwar ta bayyana hakan ne dai a wani bidiyo da mai amfani da @bethblinky ta sanya a manhajar TikTok.
Da take cigaba da bayanin halin ƙuncin data shiga, budurwar ta bayyana cewa ta sha kwashe tsawon yini guda tana sharɓar kuka sannan taji raɗaɗim abinda ya faru da ita amma daga baya duniya tayi mata karatun ta natsu.
Daga baya kuma ta nuna fuskokin tagwayen da ta haifa, inda take cewa ta yanke shawarar ta nunawa duniya su ta hanyar bayyana fuskokin su, saboda yanzu bata da saurayi.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin sharhin da mutane suka yi a kan bidiyon wanda Dimokuradiyya ta tattaro:
Nsai Chanceline ta rubuta:
“Ke jaruma ce ƴar’uwa, murnar samun yaran ki tafi raɗaɗin ƙunar ran da kika sha. Ki cigaba da jajircewa, sannan ki zama abin koyi ga yaran ki. Ina taya ki murna”
joyginikaifeanyi ta rubuta:
“Ki ƙarfafa wa kan ki guiwa sannan ki cigaba da jajircewa. Nasara na nan tafe nan gaba. Ina tayaki murna mama Ejima.”
user3478711918952 ya rubuta:
“Na tayaki murna kan ƙaruwar da kika samu ta haihuwa. Ki cigaba da jajircewa domin kan ki da yaran. Ubangiji yana tare da ke.
Kembra Geraldine ta rubuta:
“Ba zan taɓa manta halin da na shiga ba, ke jajirtacciyar mace ce. Ina taya ki murna mama.”
Bidiyon Wata Ƴar Chana Cikin Kayan Gargajiyar Ƙabilun Najeriya Ya Ɗauki Hankula
A wani labarin na daban kuma, wata ƴar Chana ta ɗauki hankulan mutane a yanar gizo bayan bayyanar wani ƙayataccen bidiyon ta.
Wata budurwa ƴar Chana ta ɗauki hankula bayan bayyanar bidiyon ta inda ta sanya kayan gargjiya na manyan ƙabilun Najeriya.
Ƴar Chanan ta bi sahun wajen yin rawa kan wata sabuwar waƙar Meghan Trainor, mai suna ‘Made You Look’ wacce ke tashi a TikTok.