Daga: Abbas Yakubu Yaura
Mai martaba Sarkin Bichi da ke jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya shirya taron addu’a domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan, musamman a yankin Arewa.
An gudanar da taron addu’ar ne a babban masallacin Bichi a ranar Juma’a, inda ya samu halartar mai martaba sarki da hakimai da malamai da kuma al’ummar masarautar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mijina Ya Sanya Mun Layoyi Akan Gadonmu Don Ya Kashe Ni, Wata ‘Yar Kasuwa Mai Neman Saki Ta Shaida Wa Kotu
Babban limamin masarautar Bichi, Khalifa Lawal Abubakar Bichi ne ya jagoranci zaman tare da yin karatun Alkur’ani mai girma, sannan ya yi addu’o’i ga shugabanni da sauran al’ummar kasar nan.
Yayin da yake addu’ar kawo karshen kalubalen tsaro, Limamin ya kuma yi addu’ar samun albarkar noma a lokacin damina, tare da neman taimakon Allah wajen tabbatar da zabe cikin lumana, ‘yanci, gaskiya da kuma sahihin zabe a 2023.
“Muna bukatar mu tuba ga Allah da neman gafararsa. Duk waɗannan suna faruwa ne sakamakon ɗabi’unmu da munanan ayyuka. Allah ya gafarta mana baki daya.” Inji babban Limamin.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala sallar, shugaban karamar hukumar Bichi, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, ya ce taron addu’ar ya zama wajibi duba da irin kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta.
Ya kuma ce yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, akwai bukatar a rika yin addu’o’in samun zaman lafiya da shugabanci na gari.
“Muna fuskantar manyan kalubalen tsaro a kasar nan, don haka ya zama wajibi a shirya irin wadannan tarukan addu’o’i domin neman zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’ummarmu.”
“Ya kuma kamata mu yi kokari mu yi addu’a domin a yi zabe lafiya a 2023,” ya kara da cewa.