By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ribas ta gano gawar wani basaraken gargajiya mai shekaru 61 a yankin Luwa dake karamar hukumar Khana ta jihar Ribas, Cif Robert Loolo.
Jami’an ‘yan sanda ne suka gano gawar marigayin a wani rafi dake da alaka da al’ummar Luwa, Bera da Bane, inda daga bisani aka sake tono shi.
Dan marigayin, Dokta Douglas Fabeke, wanda ya bayyana yadda gawar marigayin ta samu ga manema labarai, yace wasu fusatattun matasan al’umma ne suka yi masa bulala a gidansa a ranar 27 ga watan Yunin shekarar 2019 da misalin karfe 8:50 na dare kan wani matashin rikicin shugabanci daya afku.
Sannan Ya ce an biya kudin fansa sau biyu domin a sako mahaifinsa daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su da suka ki su sake shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an azabtar da basaraken ne a lokacin da aka daure shi da sanda a tsakiyar rafin, aka bar shi ya mutu ba tare da taimakonsa ba.
“Mun iya gano inda aka binne shi. Duk abin da za mu iya gane shi yana nan, mun lura an azabtar da shi. An daure shi a kan bishiya,” inji shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nnamdi Omoni, ya shaida wa wakilinmu cewa, ‘yan sandan sun gano gawarwakin wadanda suka mutu a ranar Litinin.