Jaridar Punch ta labarto cewa rundunar sojojin Nijeriya da ke yakar ta’addanci a jihar Borno ta ‘Operation Lafiya Dole’ ta garkame ofishin kungiyar yaki da yunwa wacce aka fi sani da ‘Action Against Hunger’ na jihar Borno.
Sai dai a martanin da kungiyar ta mayar, ta ce matakin da sojin Nijeriya ta dauka kan ofisoshinta, ba tare da sanarwa ko wani takamaiman bayani ba, ya sanya ta dakatar da aikin ba da tallafin ga miliyoyin ‘yan kasar.
Rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ ta ayyana kungiyar a matsayin wacce ba a maraba da ita a Nijeriya, saboda abin da ta kira cewa; kungiyar na taimakawa ‘yan ta’addan Boko Haram ne da na kungiyar ISWAP.
Sai dai ‘Action Against Hunger’ ta ce tana gudanar da aikin jin ‘kan Dan Adam ne a matsayinta na kungiya mai cin gashin kai. Kuma wacce ta kasance ‘yar ba ruwanmu, ba tare da nuna fifiko ba, ga miliyoyin al’ummar jihar Borno ta hanyar samar da muhimman ayyuka ga mutane mafi rauni, musamman mata da kananan yara.
Sanarwar da Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Ado Isa ya wallafa a shafin sada zumunta na cewa a karo da dama sojoji sun ankaras, game da irin wadannan aikace-aikace da ba su dace ba.
Sanarwar ta kuma tuhumi kungiyoyin bayar da agaji da aikata irin wadannan laifukan, ta kuma nanata haka ga kungiyoyin a lokutan wasu tarukan da suke yi.
Sanarwar ta kuma ce ta samu sahihan bayanan sirri da dama da ke nuna cewa kungiyar Action Against Hunger a matsayinta na, daya daga cikin kungiyoyin da ke harkoki a yankin arewa maso gabas.