Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Ahmadu Fintiri ya sake sabunta dokar hana fita da aka saka wa al’ummomin da ke fama da rikici a kananan hukumomin Lamurde da Guyuk na jihar Adamawa.
An kafa dokar hana fita a yankunan Waja da Lunguda na kananan hukumomin biyu biyo bayan wani kazamin rikici da ya barke kan mallakar filaye da kuma amfani da su.
KARANTA WANNAN LABARIN; https://dimokuradiyya.com.ng/shugaba-buhari-ya-yi-zazzafan-martani-kan-kisan-firaministan-japan-shinzo/
“A yau wata guda kenan da na bayar da umarnin kafa dokar hana fita a Lafiya da Boshikiri da kuma kauyukan Mumseri da Mere da Kupte da kuma Zakawon da ke kewaye da su biyo bayan rashin zaman lafiya da aka samu bayan an yi ta kokarin samar da zaman lafiya a wadannan al’ummomin.”
Fintiri ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a ta hannun sakataren yada labaran sa Humwashi Wonosikou.
“Karfe 5 na yamma zuwa karfe 6 na safe yanzu an sassauta dokar ta fara aiki daga karfe 9 na dare zuwa 6 na safe a kullum kuma sake fasalin ya fara aiki nan take,” in ji gwamnan a cikin sanarwar.
Fintiri ya kara da cewa “An samu ci gaban ne sakamakon samun zaman lafiya da aka samu a yankunan.”
Ya bukaci jami’an tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, ya kuma shawarci mazauna yankin da su ba jami’an hadin kai domin kiyaye martabar jihar Adamawa a matsayin daya daga cikin mafi zaman lafiya musamman a lokacin hutun Sallah.
Gwamnati a ranar 8 ga watan Yuni, 2022, ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomin biyu a yunkurinta na ganin an dawo da zaman lafiya bayan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.